Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.

  2. Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.

  3. Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa.

  4. Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa.

  5. Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci.

  6. Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.

  7. Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.

  8. Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa.

  9. Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”

  10. Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.

  11. Sarkin ya ba da umarnin nan ga dukan mutane, cewa, “Ku yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, yadda aka rubuta a Littafin Alkawari.”

  12. Amma a shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yosiya, aka yi Bikin Ƙetarewan nan ga Ubangiji a Urushalima.

  13. Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.

  14. Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi.

  15. Duk da haka, Ubangiji bai huce daga zafin fushinsa wanda ya ƙuna game da Yahuda saboda abin da Manasse ya aikata don yă tozarta shi ba.

  16. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan shafe Yahuda ma kamar yadda na shafe Isra’ila, daga gabana, zan ƙi Urushalima birnin da na zaɓa, da wannan haikali wanda na ce, ‘A can Sunana zai kasance.’ ”

  17. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.

  18. Ya kuma aika mugunta a gaban Ubangiji yadda kakanninsa suka yi.

  19. Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa, da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa.

  20. Ba shakka waɗannan abubuwa sun faru da Yahuda bisa ga umarnin Ubangiji domin yă kawar da su daga gabansa saboda zunuban Manasse da dukan abin da ya yi,

  21. haɗe da zub da jinin marasa laifi. Gama ya ƙazantar da Urushalima da jinin marasa laifi. Ubangiji kuwa bai yi niyyar yafewa ba.

  22. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.

  23. Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji.

  24. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi.

  25. Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.