Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  2. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

  3. Ba zan ƙara sa Isra’ilawa su fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da na ba wa bawana Musa yă umarce su.”

  4. Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.

  5. Ubangiji ya yi magana ta bakin bayinsa annabawa,

  6. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma.

  7. Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su,

  8. domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”

  9. Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

  10. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi.

  11. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.

  12. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.

  13. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,

  14. “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

  15. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,

  16. Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.

  17. Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”

  18. “Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”

  19. Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ku faɗa wa mutumin da ya aike ku wurina,

  20. ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, zan kawo masifa wa wannan wuri da kuma wa kan mutanen wurin, bisa ga dukan abubuwan da suke a rubuce a cikin littafin da sarkin Yahuda ya karanta.

  21. Domin sun yashe ni suka ƙona turare wa waɗansu alloli, suka tozarta ni da dukan gumakan da hannuwansu suka sassaƙa, fushina zai yi ƙuna a kan wannan wuri, ba kuwa zai huce ba.’

  22. Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da kalmomin da ka ji.

  23. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

  24. Saboda haka zan haɗa ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka kuma ba za su ga dukan wannan masifan da zan jawo wa wurin nan ba.’ ” Sai suka kai wa sarki abin da ta faɗa.

  25. Sai ya haura zuwa cikin haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, da na Urushalima, da firistoci, da annabawa, dukan mutane, manya da ƙanana. Ya karanta musu duk kalmomin Littafin Alkawari, wanda aka samu a haikalin Ubangiji.