Skip to content

Abijah

20 ayoyi · 9 'yan gida

An kuma san shi da: Abijam, Abia

Ayoyin da suka ambaci Abijah

  1. Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  2. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda,

  3. Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam.

  4. Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

  5. Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,

  6. Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.

  7. Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.

  8. Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki.

  9. A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda,

  10. ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce, ’yar Uriyel na Gibeya. Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam.

  11. Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.

  12. Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni!

  13. mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda.

  14. Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.

  15. Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.

  16. Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.

  17. Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida.

  18. Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.

  19. Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.

  20. Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,