Ƙidaya 31:25-47
25
Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
26
“Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi.
27
Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a.
28
Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.
29
Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji.
30
Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.”
31
Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
32
Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,000
33
shanu 72,000
34
da jakuna 61,000.
35
Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba.
36
Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne, tumaki 337,500,
37
tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne;
38
shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne;
39
jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne;
40
mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne.
41
Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
42
Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi,
43
kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne,
44
shanu 36,000,
45
jakuna 30,500
46
da mutane 16,000.
47
Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.
Settings