Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ziba

22 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”

  2. To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”

  3. Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”

  4. Sarki ya ce, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.”

  5. Saboda haka Sarki Dawuda ya umarta aka kawo shi daga gidan Makir ɗan Ammiyel, daga Lo Debar.

  6. Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”

  7. Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”

  8. Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.”

  9. Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa

  10. Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)

  11. Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki.

  12. Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne.

  13. Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu.

  14. Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.

  15. Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.”

  16. Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ”

  17. Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.” Ziba ya rusuna ya ce, “Bari in dinga samun tagomashi a gabanka ranka yă daɗe.”

  18. Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da ’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake.

  19. Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.

  20. Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau.

  21. Duk zuriyar kakana ba su cancanci kome ba sai mutuwa daga ranka yă daɗe, amma ka ba wa bawanka wuri cikin mutanen da suke ci a teburinka. Saboda haka, wanda ’yanci nake da shi da zan yi wani ƙarin roƙo a wurin sarki?”

  22. Sarki ya ce masa, “Me ya sa kake zancen nan? Ai, na riga na umarta, da kai, da Ziba ku raba filayen.”