Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Uprightness

60 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,

  2. waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,

  3. Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;

  4. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.

  5. Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.

  6. Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.

  7. Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.

  8. Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.

  9. Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.

  10. Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.

  11. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.

  12. Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.

  13. Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.

  14. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.

  15. Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.

  16. Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.

  17. Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.

  18. Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.

  19. Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.

  20. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.

  21. Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.

  22. Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.

  23. In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.

  24. Wannan ne kaɗai abin da na gane. Allah ya yi mutum tsab amma sai muka rikitar da kanmu.”

  25. Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka!