Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Second Temple: The Jews reproved for not building

5 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da The Jews reproved for not building

  1. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.

  2. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’ ”

  3. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa,

  4. “Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi da rufin katako, amma haikalin nan yana zaman kufai?”

  5. To, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku.