Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Second Temple: Gave the vessels of the first temple for

6 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da Gave the vessels of the first temple for

  1. Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.

  2. Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.

  3. Ga lissafin kayan. Manyan kwanonin zinariya guda 30 Manyan kwanonin azurfa guda 1,000 Wuƙaƙe guda 29

  4. Waɗansu kwanonin zinariya guda 30 Waɗansu kwanonin azurfa guda 410 da waɗansu kayayyaki guda 1,000

  5. Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima.

  6. Kwanonin zinariya da na azurfan gidan Allah waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga haikali a Urushalima ya kawo Babilon, a mayar da su wurinsu a haikali a Urushalima; a sa su cikin gidan Allah.