Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sadducees: Vindicated the resurrection against

18 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Vindicated the resurrection against

  1. Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.

  2. A cikinmu an yi ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa.

  3. Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.

  4. A ƙarshe, macen ta mutu.

  5. To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.

  7. Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.

  8. Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,

  9. ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”

  10. Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.

  11. To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya.

  12. Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun.

  13. A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu.

  14. To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

  15. Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?

  16. Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.

  17. Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?

  18. Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”