Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sadducees: The resurrection a cause of dispute between them and the Pharisees

4 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da The resurrection a cause of dispute between them and the Pharisees

  1. Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.”

  2. Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu.

  3. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)

  4. Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?”