Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Punishment of the Wicked: Put in slippery places

17 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da Put in slippery places

  1. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.

  2. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.

  3. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.

  4. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.

  5. Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.

  6. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.

  7. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.

  8. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.

  9. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”

  10. Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.

  11. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  12. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  13. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  14. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  15. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  16. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.

  17. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!