Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Punishment of the Wicked: Increased by neglect of privileges
Ayoyi game da Increased by neglect of privileges
“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.
Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.
Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.
Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”
“ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka.
A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku.
Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki.