Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Covenant

74 ayoyi · 24 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

  2. don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

  3. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

  4. “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

  5. don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,

  6. saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,

  7. don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

  8. Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  9. Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.

  10. Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.

  11. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.

  12. Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  13. Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.

  14. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.

  15. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,

  16. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

  17. Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,

  18. domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.

  19. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.

  20. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.

  21. Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”

  22. Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.

  23. Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.

  24. Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.