Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Covenant

74 ayoyi · 24 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan.

  2. “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,

  3. in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,

  4. zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala;

  5. amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.

  6. Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata.

  7. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,

  8. cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;

  9. zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” Sela

  10. Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,

  11. a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.

  12. Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan,

  13. waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”

  14. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  15. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji.

  16. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.

  17. Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke.

  18. Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba.

  19. Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji.

  20. Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  21. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

  22. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

  23. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

  24. cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

  25. don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,