Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tents

40 ayoyi · 24 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Isra’ilawa a cikin sansani suka ji cewa Zimri ya yi maƙarƙashiya a kan sarki, ya kuma kashe shi, sai suka yi shela, suka naɗa Omri, shugaban mayaƙa ya zama sarki a bisa Isra’ila, a wannan rana a cikin sansani.

  2. Saboda haka suka tashi, suka gudu da yamma, suka bar tentunansu, da dawakansu, da jakunansu. Suka bar sansanin yadda yake, suka gudu don su ceci rayukansu.

  3. A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.

  4. Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.

  5. Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku ’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.

  6. Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon ’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.

  7. Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.

  8. Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.

  9. Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya, kuma mutanenta suna kama da fāra. Ya miƙa sammai kamar rumfa, ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.

  10. “Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.

  11. An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke. ’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka.

  12. Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’

  13. Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.

  14. Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

  15. Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi.