- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Silas
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila.
Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”
Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”
Sa’an nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa.
A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.
Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa.
Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika ma’aikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa, “Ka saki mutanen nan.”
Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.”
Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.”
Sai ma’aikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro.
Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin.
Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ’yan’uwa suka kuma ƙarfafa su. Sa’an nan suka tafi.
Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.
Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.
Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan,
Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”
Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.
Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su.
Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa.
Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya.
Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.
Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.
Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.
Bulus, Sila da Timoti, Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi. Alheri da salama su kasance tare da ku.
Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.