Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shouting in Joy and Praise

21 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.

  2. Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu.

  3. Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace.

  4. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni.

  5. Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.

  6. Amma tsofaffin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai da yawa, waɗanda dā suka ga yadda haikali na farko yake, suka fashe da kuka mai ƙarfi sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan haikali, yayinda waɗansu kuma suka yi ihu da farin ciki.

  7. Ba wanda zai iya rabe tsakanin ihun farin ciki da na kuka, domin mutanen sun tā da murya sosai har aka ji su daga nesa.

  8. Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

  10. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

  11. Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.

  12. Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,

  13. “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”

  14. Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”

  15. Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”

  16. Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta,

  17. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.

  18. Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah,

  19. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

  20. Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko,

  21. Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.