Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shields: Many of the Israelites used, with expertness

5 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Many of the Israelites used, with expertness

  1. Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.

  2. Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;

  3. mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;

  4. Asa ya kasance da mayaƙa dubu ɗari uku daga Yahuda, kintsatse da manyan garkuwoyi da māsu, da kuma mayaƙa dubu ɗari biyu da dubu tamanin daga Benyamin, riƙe da ƙananan garkuwoyi da kuma baka. Dukan waɗannan jarumawa ne ƙwarai.

  5. Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa.