Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Denial: Becomes strangers and pilgrims
Ayoyi game da Becomes strangers and pilgrims
Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.
Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu.
Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa.
Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.