Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Denial: Preferring the profit of others
Ayoyi game da Preferring the profit of others
Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.
Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.
Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.
kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.