- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Secretary
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare;
Adoniram kuwa shi ne shugaban aikin gandu; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubucin tarihi;
Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.
Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.
Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,
masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.
Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.
Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.
Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.
Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.
A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,
“Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.
Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,
wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin.
Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”
Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.
Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”
Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.
Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa.
Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,
“Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”
Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.
Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin.
Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci. Yehiyel ɗan Hakmoni ne ya lura da ’ya’yan sarki maza.
Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa.