Tsallake zuwa abun ciki

Ahikam

20 ayoyi · 4 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ahikam

  1. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,

  2. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  3. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zaɓi Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan yă zama shugaban sauran mutanen da suka rage a Yahuda.

  4. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.

  5. Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba.

  6. suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa.

  7. Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi.

  8. Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar.

  9. Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba,

  10. Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa. Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani.

  11. Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu,

  12. suka ce masa, “Ba ka san cewa Ba’alis sarkin Ammonawa ya aiki Ishmayel ɗan Netaniya ya ɗauke ranka ba?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam bai gaskata su ba.

  13. Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, “Kada ka yi irin wannan abu! Abin da kake faɗa game da Ishmayel ba gaskiya ba ne.”

  14. A wata na goma sha bakwai sai Ishmayel ɗan Netaniya, ɗan Elishama, wanda yake mai jinin sarauta yake kuma ɗaya daga cikin hafsoshin sarki, ya zo tare da mutum goma wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa. Yayinda suke ci tare a can,

  15. sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutum goma waɗanda suke tare da shi suka kashe Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da takobi, suka kashe wannan da sarkin Babilon ya naɗa a matsayin gwamna a kan ƙasar.

  16. Ishmayel ɗan Netaniya ya fito daga Mizfa don yă sadu da su. Sa’ad da ya sadu da su, sai ya ce, “Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam.”

  17. Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.

  18. Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon

  19. don su kuɓuce wa Babiloniyawa. Sun ji tsoronsu domin Ishmayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babilon ya naɗa gwamna a kan ƙasar.

  20. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.