Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Achbor

7 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.

  2. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  3. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

  4. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.

  5. Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane.

  6. sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa.

  7. Ko da yake Elnatan, Delahiya da Gemariya sun roƙi sarki kada yă ƙone littafin, bai saurare su ba.