Tsallake zuwa abun ciki

Hilkiah

20 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Hilkiah

  1. “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

  2. Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.

  3. Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.

  4. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,

  5. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  6. Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.

  7. Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.

  8. Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,

  9. Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;

  10. Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima.

  11. Yayinda suke fitar da kuɗin da aka kai cikin haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya sami Littafin Dokar Ubangiji da aka bayar ta wurin Musa.

  12. Hilkiya ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a cikin haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan.

  13. Sa’an nan Shafan magatakarda ya sanar da sarki ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta daga cikinsa a gaban sarki.

  14. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.

  15. Hilkiya tare da waɗanda sarki ya aika, suka tafi suka yi magana da annabiya Hulda, wadda take matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai tsaron wurin ajiyar riguna. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  16. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku.

  17. Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya,

  18. da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,

  19. Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.

  20. Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,