Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Secret

23 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma ’ya’yanmu har abada.

  2. Sa’ad da kuma masifu masu yawa da wahaloli masu yawa suka auko musu, wannan waƙa za tă zama shaida a kansu, domin zuriyarsu ba za tă manta da ita ba. Na san abin da za su iya yi, kafin ma in kawo su cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa.”

  3. Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”

  4. “Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka.

  5. “ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni.

  6. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.

  7. da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?

  8. Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.

  9. In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,

  10. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.

  11. amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,

  12. Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”

  13. Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

  14. don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

  15. Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

  16. “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

  17. Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili.

  18. “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.

  19. Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.

  20. Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.

  21. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

  22. Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.

  23. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.