Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanitation

289 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.

  2. Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.

  3. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

  4. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

  5. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.

  6. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.

  7. In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.

  8. Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.

  9. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.

  10. Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.

  11. In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.

  12. Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.

  13. “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.

  14. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  15. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.

  16. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.

  17. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.

  18. “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.

  19. Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ”

  20. “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.

  21. A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.

  22. Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.

  23. In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.

  24. “Sa’ad da wani yana da kumburi, ko ɓamɓaroki, ko tabo a fatar jikinsa da zai iya zama cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga Haruna firist, ko kuwa ga ɗaya a cikin ’ya’yansa maza wanda yake firist.

  25. Firist zai bincika mikin da yake a fatar mai cutar, in gashin a mikin ya juya ya zama fari, mikin kuma ya zama kamar ya fi zurfin fatar jiki, wannan cutar kuturta ce. Sa’ad da firist ya bincike shi, zai furta shi marar tsarki.