Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanitation: Penalties concerning

10 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da Penalties concerning

  1. Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku.

  2. Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za tă manne muku, tă cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.

  3. Ubangiji zai buga ku da cuta mai lalacewa, da zazzaɓi, da ƙuna, da zafin rana, da fāri, da burtuntuna, da fumfuna, waɗanda za su azabtar da ku sai kun hallaka.

  4. Ubangiji zai buge ku da maruran Masar, da ƙazuwa, da kuma ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba

  5. Ubangiji zai buge gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai masu zafi da ba za a iya warkar da su ba, za su yaɗu daga tafin ƙafafu zuwa bisa kanku.

  6. Dukan waɗannan la’anoni za su sauko a kanku. Za su bi ku, su same ku, sai an hallaka ku, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da ya ba ku ba.

  7. Ubangiji zai aika da annoba masu zafi a kanku da zuriyarku, masifu masu zafi waɗanda za su daɗe, da mugayen cututtuka waɗanda ba sa kawuwa.

  8. Zai kawo muku dukan cututtukan Masar da kuke tsoro, za su kuwa manne muku.

  9. Ubangiji kuma zai kawo muku kowane irin ciwo da masifar da ba a rubuta a cikin wannan Littafin Doka ba, har sai an hallaka ku.

  10. Ku da kuke da yawa kamar taurari a sarari za ku ragu ku zama kaɗan, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba.