Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanitation: Carcases

31 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da Carcases

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi.

  2. Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”

  3. Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.

  4. “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.

  5. Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.

  6. “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu.

  7. Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.

  8. Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.

  9. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.

  10. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.

  11. In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.

  12. Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.

  13. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.

  14. Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.

  15. In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.

  16. Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.

  17. “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.

  18. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  19. “ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,

  20. duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.

  21. Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana

  22. “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.

  23. “Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.

  24. Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba.

  25. Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.