Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanitation: Filth, disposition of

17 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da Filth, disposition of

  1. Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.

  2. In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.

  3. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,

  4. wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.

  5. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.

  6. Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum.

  7. Duk naman hadayar da ya rage har kwana uku, dole a ƙone shi.

  8. “ ‘Ba za a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki ba; dole a ƙone shi. Game da sauran nama, kowa da yake mai tsarki zai iya ci.

  9. Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  10. Sa’an nan ku ƙone sauran naman da kuma burodin.

  11. Naman da fatar kuwa ya ƙone waje da sansanin.

  12. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone.

  13. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.

  14. Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi.

  15. Ku keɓe wuri waje da sansani inda za ku iya zuwa don yin bayan gari.

  16. Sai ku ɗauki wani abin tona ƙasa, sa’ad da kuka yi bayan gari, sai ku tona rami, ku rufe bayan garinku.

  17. Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani.