Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rome: Christians in:

22 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Christians in:

  1. Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.

  2. Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.

  3. Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.

  4. Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.

  5. Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.

  6. Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.

  7. Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.

  8. Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.

  9. Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.

  10. Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ’yan’uwan da suke tare da su.

  11. Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.

  12. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.

  13. Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.

  14. To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara.

  15. Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi.

  16. Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.

  17. Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi.

  18. Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara.

  19. Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.

  20. Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki. I, zan kuwa ci gaba da farin ciki,

  21. Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

  22. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa.