Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prisoners: John the Baptist

13 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da John the Baptist

  1. Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa

  2. To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus,

  3. gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.”

  4. Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne.

  5. A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai,

  6. har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa.

  7. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”

  8. Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa

  9. ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku.

  10. Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta.

  11. Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.

  12. Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura.

  13. Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.