Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Philosophy

90 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.

  2. Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.

  3. “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.

  4. Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?

  5. Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

  6. A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

  7. mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,

  8. don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,

  9. don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.

  10. “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

  11. yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

  12. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

  13. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

  14. Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,

  15. yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’

  16. Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.

  17. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.

  18. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

  19. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’

  20. “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.

  21. Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.

  22. Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.

  23. Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.

  24. gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi.

  25. Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.