Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Philosophy

90 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.

  2. Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.

  3. Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.

  4. Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.

  5. Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.

  6. Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.

  7. Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.

  8. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

  9. Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.

  10. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

  11. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.

  12. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.

  13. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  14. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

  15. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?

  16. Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?

  17. Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne

  18. da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?

  19. Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.

  20. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?

  21. Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?

  22. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

  23. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?

  24. Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.

  25. “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.