Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paran: Desert or wilderness of

6 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Desert or wilderness of

  1. Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.

  2. Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran.

  3. Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.

  4. Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.

  5. Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar.

  6. Waɗannan su ne kalmomin da Musa ya yi wa dukan Isra’ila, a hamada gabas da Urdun, wato, Araba, ɗaura da Suf, tsakanin Faran da Tofel, Laban, Hazerot da Dizahab.