Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Missionary Work By Ministers: Obligations to engage in

6 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da Obligations to engage in

  1. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.

  2. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”

  3. Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.

  4. Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci.

  5. Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma.

  6. Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!