Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Missionary Work By Ministers: Warranted by predictions concerning the heathen, &c

4 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da Warranted by predictions concerning the heathen, &c

  1. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.

  2. Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.

  3. Bari su ɗaukaka Ubangiji su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.

  4. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.