Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Missionary Work By Ministers: Aid those engaged in

7 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da Aid those engaged in

  1. Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.

  2. Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.

  3. Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.

  4. Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka.

  5. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah.

  6. Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba.

  7. Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan.