Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Meshullam

24 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,

  2. ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu.

  3. Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.

  4. Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber,

  5. Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa;

  6. Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.

  7. Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;

  8. Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer.

  9. Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi,

  10. Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.

  11. Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu.

  12. Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.

  13. Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare.

  14. Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.

  15. Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa.

  16. Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.

  17. da Meshullam, da Abiya, da Miyamin,

  18. da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,

  19. Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya,

  20. da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,

  21. na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan;

  22. na iyalin Iddo, Zakariya; na iyalin Ginneton, Meshullam;

  23. Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.

  24. tare da Azariya, Ezra, Meshullam,