Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Land

123 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.”

  2. Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.

  3. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.

  4. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.

  5. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.

  6. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.

  7. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.

  8. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,

  9. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  10. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  11. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.

  12. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.

  13. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.

  14. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.

  15. Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne.

  16. In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna.

  17. Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta.

  18. In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa.

  19. In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba.

  20. Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.

  21. “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,

  22. firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.

  23. A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.

  24. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.

  25. Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce,