Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Instruction

179 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.

  2. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.

  3. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.

  4. Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,

  5. gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.

  6. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.

  7. Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege.

  8. Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.

  9. Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba.

  10. Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.

  11. Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.

  12. Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka.

  13. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.

  14. Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka.

  15. Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka.

  16. Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.

  17. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.

  18. Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.

  19. Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba.

  20. Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.

  21. Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka.

  22. Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.

  23. Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.

  24. Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.

  25. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.