Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Instruction

179 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.

  2. Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.

  3. Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.

  4. Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka.

  5. Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.

  6. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.

  7. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.

  8. Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.

  9. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.

  10. Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.

  11. Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!

  12. Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.

  13. Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.

  14. Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.

  15. Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.

  16. Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.

  17. Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba.

  18. Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.

  19. Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata.

  20. Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe.

  21. Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.

  22. Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.

  23. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!

  24. Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.

  25. Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.