Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Instruction

179 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.

  2. Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.

  3. Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.

  4. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.

  5. Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu.

  6. Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.

  7. Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.

  8. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.

  9. Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.

  10. Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.

  11. Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.

  12. Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.

  13. Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya.

  14. Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.

  15. Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”

  16. Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.

  17. Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?

  18. Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.

  19. Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.

  20. Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.

  21. Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.

  22. Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.

  23. Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.

  24. Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.

  25. Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana.