Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Instruction: General references
Ayoyi game da General references
Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.