Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Death: Of the righteous

31 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Of the righteous

Tace bisa littafi
  1. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

  2. Saboda haka zan haɗa ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka kuma ba za su ga dukan wannan masifan da zan jawo wa wurin nan ba.’ ” Sai suka kai wa sarki abin da ta faɗa.

  3. Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta.

  4. Waɗanda suke aikata abin da yake daidai sukan shiga da salama; sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.

  5. Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai.

  6. In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne.

  7. Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne,

  8. ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne,

  9. ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

  10. Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu

  11. farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.

  12. Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan.

  13. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”

  14. “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?”

  15. Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.

  16. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  17. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.

  18. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,

  19. Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.

  20. Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce.

  21. Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba;

  22. amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki.

  23. ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.

  24. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.

  25. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.