Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Death: Of the wicked

48 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Of the wicked

Tace bisa littafi
  1. “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,

  2. mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.

  3. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?

  4. Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?

  5. Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,

  6. jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.

  7. Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.

  8. Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su.

  9. Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.

  10. Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.

  11. Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.

  12. Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.

  13. Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”

  14. Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

  15. gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

  16. Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.

  17. A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba.

  18. Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,

  19. amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.

  20. da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.

  21. Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.

  22. zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.

  23. Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.

  24. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.

  25. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.