Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Commandments

394 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

  2. Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

  3. Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba.

  4. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.

  5. Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)

  6. Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

  7. Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.

  8. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  9. Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

  10. Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!

  11. Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’

  12. Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah),

  13. sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu.

  14. Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”

  15. Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.

  16. Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”

  17. If any man have ears to hear, let him hear.

  18. Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali.

  19. Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi.

  20. Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)

  21. Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi.

  22. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,

  23. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.

  24. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  25. Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.