Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Altars

89 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ahab ya gina ginshiƙin Ashera, ya kuma aikata abubuwa masu yawa don yă tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila da suka riga shi.

  2. Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden.

  3. Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo.

  4. Da sarki ya dawo daga Damaskus ya ga bagaden, sai ya tafi kusa da shi ya kuma miƙa hadaya a bisansa.

  5. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.

  6. Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.

  7. Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma.

  8. Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah. Bagaden zinariya; teburin da ake ajiye burodin Kasancewa;

  9. Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah.

  10. Duk da tsoron da suke ji na mutanen da suke kewaye da su, sun gina bagaden a wurinsa, suka kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagaden ga Ubangiji safe da yamma.

  11. mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali;

  12. Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”

  13. Babiloniyawan da suke yaƙi da wannan birni za su zo ciki su cinna masa wuta; tare da gidaje inda mutane suka tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙona turare a rufin ɗakuna wa Ba’al suka zub da hadayun sha wa waɗansu alloli.

  14. Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu, Ga Allahn da ba a sani ba. To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.