Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 20:28kusan 33 M.

    Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”

  2. Yohanna 20:29kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”

  3. Yohanna 20:30kusan 33 M.

    Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.

  4. Yohanna 20:31kusan 33 M.

    An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

  5. Yohanna 21:1kusan 33 M.

    Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.

  6. Yohanna 21:2kusan 33 M.

    Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.

  7. Yohanna 21:3kusan 33 M.

    Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.

  8. Yohanna 21:4kusan 33 M.

    Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.

  9. Yohanna 21:5kusan 33 M.

    Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?” Suka amsa suka ce, “A’a.”

  10. Yohanna 21:6kusan 33 M.

    Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.

  11. Yohanna 21:7kusan 33 M.

    Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.

  12. Yohanna 21:8kusan 33 M.

    Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne.

  13. Yohanna 21:9kusan 33 M.

    Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.

  14. Yohanna 21:10kusan 33 M.

    Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”

  15. Yohanna 21:11kusan 33 M.

    Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.

  16. Yohanna 21:12kusan 33 M.

    Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.

  17. Yohanna 21:13kusan 33 M.

    Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.

  18. Yohanna 21:14kusan 33 M.

    Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.

  19. Yohanna 21:15kusan 33 M.

    Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”

  20. Yohanna 21:16kusan 33 M.

    Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”

  21. Yohanna 21:17kusan 33 M.

    Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.

  22. Yohanna 21:18kusan 33 M.

    Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”

  23. Yohanna 21:19kusan 33 M.

    Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”

  24. Yohanna 21:20kusan 33 M.

    Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)

  25. Yohanna 21:21kusan 33 M.

    Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”