circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yohanna 10:39kusan 33 M.
Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
- Yohanna 10:40kusan 33 M.
Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna
- Yohanna 10:41kusan 33 M.
mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”
- Yohanna 10:42kusan 33 M.
A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.
- Yohanna 11:1kusan 33 M.
To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta.
- Yohanna 11:2kusan 33 M.
Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta.
- Yohanna 11:3kusan 33 M.
Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
- Yohanna 11:4kusan 33 M.
Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”
- Yohanna 11:5kusan 33 M.
Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus.
- Yohanna 11:6kusan 33 M.
Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
- Yohanna 11:7kusan 33 M.
Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
- Yohanna 11:8kusan 33 M.
Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
- Yohanna 11:9kusan 33 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan.
- Yohanna 11:10kusan 33 M.
Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
- Yohanna 11:11kusan 33 M.
Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
- Yohanna 11:12kusan 33 M.
Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.”
- Yohanna 11:13kusan 33 M.
Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
- Yohanna 11:14kusan 33 M.
Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu,
- Yohanna 11:15kusan 33 M.
amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
- Yohanna 11:16kusan 33 M.
Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
- Yohanna 11:17kusan 33 M.
Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.
- Yohanna 11:18kusan 33 M.
Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima,
- Yohanna 11:19kusan 33 M.
Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu.
- Yohanna 11:20kusan 33 M.
Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
- Yohanna 11:21kusan 33 M.
Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.