Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 11:22kusan 33 M.

    Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”

  2. Yohanna 11:23kusan 33 M.

    Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”

  3. Yohanna 11:24kusan 33 M.

    Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”

  4. Yohanna 11:25kusan 33 M.

    Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;

  5. Yohanna 11:26kusan 33 M.

    kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”

  6. Yohanna 11:27kusan 33 M.

    Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”

  7. Yohanna 11:28kusan 33 M.

    Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”

  8. Yohanna 11:29kusan 33 M.

    Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa.

  9. Yohanna 11:30kusan 33 M.

    Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.

  10. Yohanna 11:31kusan 33 M.

    Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.

  11. Yohanna 11:32kusan 33 M.

    Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”

  12. Yohanna 11:33kusan 33 M.

    Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.

  13. Yohanna 11:34kusan 33 M.

    Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”

  14. Yohanna 11:35kusan 33 M.

    Yesu ya yi kuka.

  15. Yohanna 11:36kusan 33 M.

    Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”

  16. Yohanna 11:37kusan 33 M.

    Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”

  17. Yohanna 11:38kusan 33 M.

    Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse.

  18. Yohanna 11:39kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”

  19. Yohanna 11:40kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”

  20. Yohanna 11:41kusan 33 M.

    Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni.

  21. Yohanna 11:42kusan 33 M.

    Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”

  22. Yohanna 11:43kusan 33 M.

    Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”

  23. Yohanna 11:44kusan 33 M.

    Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”

  24. Yohanna 11:45kusan 33 M.

    Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.

  25. Yohanna 11:46kusan 33 M.

    Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.